menu icon
AREWA BOOKS
Login
Search for a book

Frequently Asked Questions!

YAYA AREWABOOKS TAKE AIKI NE?

ArewaBooks zata bawa marubuci damar wallafa/rubuta littafansa akan tsarin Parts/Chapters, sannan yana da ikon saka littafinsa a Free ko Paid akan kowani Chapter/Part.

Sannan dakwai tsarin Followers/Following wanda wannan zaibawa mabiyanku/makaranta damar Following dinku, aduk sanda kuka wallafa littafi/Chapter zasu samu sanarwa (Notification) ta saman wayoyinsu.

TAYAYA ZAMU GA CINIKAIYARMU?

Acikin ArewaBooks akwai bayyanannen asusu (wallet) har kala biyu. Earning da Recharge/Refill.

EARNING - itace ta masu wallafa littafai duk Chapter da aka saye kudin zai shiga wannan asusun (wallet).

RECHARGE/REFILL - asusu ce ta makaranta kafin su iya sayen littafanku sai sunfara saka kudi ta ArewaBooks account dinsu, tau duk kudin da zasu saka acikin wannan asusun zai bayyana.

TOH TAYAYA MAKARANTA ZASU SAKA KUDI?

ArewaBooks ta saukaka hanyar da makaranta zasu saka kudi domin sayayyar littafan da suke muradi, har hanyoyi uku.

  • Katin Banki (Debit/Credit Card) - Paystack gateway
  • Local Bank Transfer - USSD, POS etc.
  • Katin waya (Airtime transfer) - MTN, AIRTEL, GLO & 9MOBILE.
TAYAYA KUKE BIYAN MARUBUTA IDAN AN SAYE LITTAFANSU?

Dazarar asusun Earning (wallet) din marubuci takai 2,000 ko sama da hakan, a lokacin yake da damar mallakar kudinsa (withdrawal request). ArewaBooks zata aika masa kudin (payment) cikin lokaci kankani.

YAYA TSARON (Security) LITTAFANMU A AREWABOOKS?

ArewaBooks tayi kokarin samar da tsaro (security) ga littafai... A shafinmu (website) ko Manhaja (Application) babu damar wani ya danne rubutun har yayi copy/share.

Sannan ArewaBooks tazo muku da wata tsarin kare littafanku daga barayin yanargizo ta hanyar zabar "Platform Specific"... Shi Platform Specific zaibawa marubuci damar zabar inda yakeson littafinsa ya bayyana kamar:

  • All (Web and App)
  • App Only

All (Web and App) - idan ka zaba wannan yayin saka littafinka, tau zai bayyana duka a shafi (website) da Manhaja (Application).

App Only - idan ka zaba wannan yayin saka littafi, tau zai bayyana ne kadai acikin Manhaja (Application) wanda shine zaikarawa littafin tsaro (security) idan yana cikin Manhaja ne kadai.

Note: "App Only" yana rage yawan samun makarantar littafi, sai kayi tunanin wanne kafi bukata yawan security ko yawan makaranta.

INADA MABIYA DA YAWA A WATTPAD/WHATSAPP/FACEBOOK, TAYAYA KENAN ZANJANYOSU AREWABOOKS?

Ehh, Akwai hanyoyi/dabaru da dama, Amma zamu bada guda daya zuwa biyu.

Idan ka bude account a ArewaBooks shine kayi kokarin dora tsofaffin littafanka aciki. Ko suna Wattpad ko basa Wattpad kafara wannan kokarin.

Sannan sai kayi sanarwa a account dinka na Wattpad da sauran kafafar sadarwa WhatsApp/Facebook/Telegram da sauransu, da yawa mabiyanka zasu samu wannan sakon, har suyi following dinka a ArewaBooks.

Sannan zaka iya fara sabon littafi a Wattpad account naka, sai aciki kayi sanarwan cigaban zaikasance a ArewaBooks. Haka zalika zaka iya cire karshen tsofin littafanka dasuke wattpad abar iya farkon, sai cikkaken yakasance a ArewaBooks account naka. Tabbas da yawan mabiyanka zasu biyoka suyi following naka a ArewaBooks.

MEYASA AREWABOOKS?

Mun kirkiri wannan shafin/manhaja ArewaBooks ne duba da irin halin da marubutan Arewa suke ciki ta kasuwancin littatafai ayanzu. Matsalar ta shafi kowa daga masu bugawan da masu wallafawa a yanargizo (online), Masu bugawan basu samun kasuwa kamar dacan kasancewar zuwan yanargizo (online), sai yazamana anfi amfani da wayar salula agun karatun littafai ayanzu. Sai marubutan da yawa suka dawo online saidai kash babu inda zasu siyar da littafan nasu cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Da yawa suna sayarwa a WhatsApp ne, wasu kuwa a Free sukeyi badan komai ba sai dan son rubutun a jininsu yake shine muradinsu, wasu kuwa hakura suke da rubutun saboda takaicin canzawar yanayin.

Wadannan sune kadan daga cikin dalilin dayasa aka samar da ArewaBooks.